Yanzu-Yanzu

Jajantawa “yan Kasuwar Singa dake cikin birnin Kano – Aminu Ado

 

By: Mukhtar Yahaya Shehu

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, JP, ya jajantawa “yan Kasuwar Singa dake cikin birnin Kano bisa iftila’in gobara data tashi a kasuwar

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun sakataren yada labarai na Masarautar Abubakar Balarabe Kofar Naisa Wanda kuma ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa Mai Martaba Sarkin ya nuna damuwarsa matuka a lokacin da ya samu labarin tashin gobarar.

Haka kuma Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake mika sakon jajantawa ga “yan Kasuwar Kurmi da Kasuwar Rimi bisa ifila’in Gobara da suka samu a kwanakin baya.

Sarkin ya tayasu jajantawa da nuna alhini, inda yayi addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan anan gaba.

Yayi kira kira ga yankasuwar da kungiyoyin yan Kasuwa su cigaba da yawaita adduo’oi da kuma daukar dukkan matakan kare kiyaye afkuwar irin wannan iftila’I a koda yaushe.

 

Leave a Comment