Da Dumi-Dumi

JAHAR KANO: Zamu Tallafawa Matan Sojoji

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya Sha alwashin tallafawa yara da matan tsofaffin sojojin da suka mutu.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan a yayin bikin tunawa da tsofaffin sojoji Wanda aka fi Sani da ‘yan mazan jiya.

Ya ce, gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta kula da harkokin walwala da jin dadin rayuwar matan sojoji da mazajensu suka rasa rayukansu wajen aikin soji.

Shima ana sa jawabin, shugaban tsofaffin sojojin na Jihar Kano Kabiru Isyaku ya bayyana cewar fiye da shekaru goma sha biyar shugabancin kula da harkokin tsofaffin sojoji na Kano na fuskantar kalubale da dama inda yake rokon gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf zata waiwayesu.

Mun sami Karin wannan sanarwar daga wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano Adamu Dabo ne a yayin bikin na bana, manyan shuwagabanin harkokin tsaro dake fadin jihar Kano sun samu halattar taron.

Leave a Comment