Labaran Jiha

JAHAR KANO: Zamu Hada Hannu Da Limaman Kano Domin Samun Cigaba A Fadin jihar Kano

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin jihar Kano ta yi Kira ga malam jihar Kano da su hada hannu da gwamnati wajen addu’oin kawo zaman lafiya ga jihar Kano.

Kiran ya fitone daga bakin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a yayin wani taro na musamman da gwamna yayi da limaman jihar Kano Wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya ce malamai su ne yakamata a ce suna yawan fadakarwa akan harkokin tarbiyar al’umma akullum Bawai su shiga harkokin siyasa ba.

Ya kuma ce duk lokacin da wata matsala ta taso ya kamata malami su hau mambari domin fadakar da al’umma bisa yadda gakiyar lamari yake.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano Adamu Dabo ya bamu labarin cewar a yayin taron akwai mataimakin gwamnan jihar Kano kwamrade Aminu Abdulsalam kwamishinonin gwamnati shugaban limaman jihar Kano da sauran manyan limaman jihar Kano.

Leave a Comment