Labaran Jiha

JAHAR KANO: Tabbatar Da Adalci A Kotu Ya Kara Kawo Martabar Alkalai A Idon Jama’a

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Kwarewa da tabbabatar da adalci da alkalan kotun kolin kasar nan suka yi wajen yanke hukuncin shari’ar jahar Kano ya kara dawo da martabar fannin shari’a da sauran alkalai a idon duniya.

Shugaban hukumar bada shawara da jagoranci na jihar Kano Hon. Faruk Abdu Sumaila ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai dake a fadar gwamnati.

Faruk Sumaila yace, lokacin da aka bashi jagorancin wannan hukuma ya sameta a yanayi mara dadi na halin ko in kula, amma da shigowarsa hukumar, yayi kokarin hada kan ma’aikatansa don yin aiki tare, ba tare da wata tsangwama ba.

Ya kuma kara da cewa, zuwansa wannan hukuma gwamna Abba Kabir ya bada umarnin fidda kudade da kayan aiki wadanda aka taimakawa sojoji dasu domin daukar horo don kara masu karfin gwuiwa, inda yace wannan abin a yabawa gwamnati ne .

Ya kuma bukaci al’ummar jihar Kano dasu yi kokarin samun takardar shaidar zama dan jihar Kano domin irin muhimmancin da take da ita ya kuma bayyana cewa kafin a yi maka wannan shaidar takardar sai an tabbatar da cewa dan jihar Kano ne kafin a tabbatar maka da ita.

Abdu Sumaila yace, sun gudanar da taron matasa don wayar musu da kai da kuma basu shawara wajen sanin mahimmmanci cigaba da neman ilimi musamman a matakin gaba da sakandire.

Daga bisani, Faruk Abdu Sumaila yace nan bada dadewa ba zasu yi shirin da zai karade kananan hukumomi 44 da muke dasu a wannan jiha tamu dan tabbatarwa da al’umma kusancin su da wannan hukuma don sama masu ayyukan yi musamman na tsaro wajen shige masu gaba akan abinda suke da burin zama don kyautata rayuwarsu .

Leave a Comment