Labaran Jiha

JAHAR KANO: Kula Da Rayuka Da Dukiyar Al’umma Shine Aikin Jami’an Tsaro

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci jami’an tsaro su tsaya tsayin daka wajen aiwatar da ayyukan tsaro a fadin jihar nan.

Gwamna Yusuf ya bukaci hakan yayin bikin yaye Sabin jami’an tsaro da aka horar guda 177 ashelikwatar jami’an tsaro na civil defense dake rukunin gidajen kwankwasiya city dake karamar hukumar kunbutso.

Gwamna Yusuf ya ce tsaron al’umma wajibi nedan haka gwamnati da jami’an tsaro dole su hada hannu guri guda domin samarwa al’umma kariya da Kuma dukiyarsu.

Tun da fari, anasa jawabin, shugaban jami’an tsaro na civil defense na jahar Kano Muhammad Lawan falala ya ja hankalin sabbin jami’an ga cewar Yan zu daban suke da sauran al’umma don haka kare dokiyar al’umma da rayukansu shi yakamata susa agaba.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano Adamu Dabo ya bamu labarin cewar a yayin bikin yaye Sabin jami’an tsaro akwai sakataran gwamnati jahar Kano Dr.Abdullahi Baffa Bichi da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kano Shehu wada sagagi da kwamishinonin gwamnati jahar Kano

Leave a Comment