Labaran Jiha

JAHAR KANO: Gwamnatin Kano Ta Biyawa Dalibai 6,500 Kudin Jamb

Written by Admin

Daga: Adamu Dabo

Gwamnatin jahar Kano ta biyawa dalibai dubu shida da dari biyar kudin jarabawar JAMB domin inganta harkokin ilimin dalibai Jahar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci bayar da tallafin ga dalibai 6,500 a dakin taro na coronation dake Gidan gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya ce ya zama wajibi gwamnati ta tallafawa dalibai Jahar Kano domin ‘ya’yanmu Basu da wani gata da ya wuce gwamnatin jihar Kano ta kula da ilimin su da rayuwarsu ta yau da kullum.

Yusuf ya Kuma ce tun baya da aka zabe shi amatsayinsa na Gwamna, gwamnatisa ta awaitar da abubuwa na Alkhairi a fagen ilimin daliban jahar Kano.

Shima a nasa jawabin kwamishinan ilimi Alhaji Haruna Umar Doguwa ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf wajen taimakon ilimi a fadir jahar Kano.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano Adamu Dabo ya rawaito cewar a yayin taron akwai mataimakin gwamnan jihar Kano kwamrade Aminu Abdulsalam,sakataran gwamnati jahar Kano Dr.Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinoni da shuwagabannin kananan hukumomi.

Leave a Comment