Labaran Jiha

JAHAR KANO: Gwamnatin Jahar Kano Ta Rantsar Da Alkalai Tara Da Kadi Hudu

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci bangaran shari’a da su ringa kwatanta gaskiya da Amana wajen gudanar da ayyukansu na shari’a.

Bukatar hakan ta fitone da bakin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yayin da ya jagoranci rantsar da sabbin manyan alkalai guda Tara da Kuma kadi na kotun shari’ar musulunci guda hudu Wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya ce, duk lokacin da aka yi gaskiya a harkar shari’a to al’umma zasu samu daidaito a duk al’amuransu na yau da kullum.

Manyan alkalan da aka rantsar sun hada da Barista Fatima Adam, Barista Hauwa Lawan, Barista Musa Ahmad, Barista farida rabiu Danbaffa, Barista Musa Dahuru Muhammad, barista halima Aliyu Nasir, barista Aisha Mahmud, Barista Adamu Abdullahi da Kuma Barista Hanif Sunusi Yusuf haka zalika akwai alkalai na kotun shari’ar musulunci guda hudu Wanda suka hada da Muhammad Adamu Kademi, Salisu Muhammad, Isah Idris said da Kuma Aliyu Muhammad.

Kwamishinan shari’a na jahar Kano barista Haruna Isah Dederi shine ya jagoranci rantsuwar.

Wakilinmu ya ruwaito cewar a yayin bikin rantsuwar akwai kwamishinonin gwamnati da manyan kusoshi a harkar shari’a.

Leave a Comment