Ilimi

IYAYE SU ZAGE DANTSE WAJEN ILMANTAR DA ‘YA’YANSU

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Hukumar Gudanarwa ta makarantar MADARASATUL AHBABUL MUSDAFA Islamiyaya dake unguwar gobirawa bayan makarantar madaki A karamar hukumar Dala, ta shawarci dalibai da su kasance masu amfani da ilimin da suka samu ta hanyoyin da suka dace, domin tsira a gobe Alkiyama.

Shugaban makarantar malam Sunusi Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai Jim-kadan bayan kammala saukar karatun Al’kurani mai girma wanda daliban makarantar kimanin mutanen 40 suka yi a ɗakin taro nasa’adu zungur dake gwammaja anan birnin Kano.

Mal. Sunusi Abubakar yace amfanin ilimi a gurin ɗan Adam shine ya riƙa amfani dashi domin bautawa Allah Subahanahu Wata’ala da aiwatar da shi a cikin rayuwarsa ta yau da kullum, inda yace ilimi yana ɗaya daga cikin abubuwan dake setawa Al’umma rayuwar su.

Anasa ɓangaran dagacin gobirawa mal. Musa Isa muhammad yayi kira ga masu ruwa da tsaki da mahukunta da masu hannu da shuni dasu kasance masu taimakawa irin waɗan nan makarantu domin ciyar da harkokin ilimi gaba kasancewa ilimi shine kan gaba wajen ingata rayuwar al’umma.

Kazalika shima a nasa ɓangaren Labaran Sani Adakawa chanchanta, wakilin ɗan majalisar tarayya na ƙaramar hukumar Dala, Aliyu sani madaki ya yabawa malaman kan irin ƙoƙarin da suke naganin sun ɗora al’umma akan hanyar data dace, ya ƙara da cewa ƙofar su a buɗe take domin tallafawa harkokin adinin musulinci takowace fuska.

Ɗaliban sun sha alwashin yin amfani da ilimin da suka samu wajan yin biyayya ga Allah subahanahu wata’ala da taimakawa sauran ɗalibai ƴan baya.

Ayayin taron saukar an ƙaddamar da wani sabon litafi mai ɗauke da bayanai daban daban dasuka ƙunshi zamantakewa tarayuwa musamman a ɓangaran daya shafi zamantakewar aure, an gudanar da nasihohi da dama daga bakin manƴan malamai daban daban.

Leave a Comment