Da Dumi-Dumi

Iyaye su tabbata sun maida Dalibai Makarantu a ranakun Lahadi da Litinin masu zuwa – Abdu Yalo

From: KABI GETSO

Shugaban Malaman Makarantun Sakandire na kasa reshen Jihar Kano Kwamared Abdu Usman Yalo, ya shawarci iyaye da su tabbata sun maida ‘ya’yansu Makarantu a ranakun da aka ware don komawa aiki.

Kwamared Yalo wanda kuma shine sakataran Kungiyar TUC ta Jihar Kano, kuma Babban Mai binciken kudi na kungiyar Malaman Makarantun Sakandire na kasa baki daya.

Yalo yayi wannan jawabin ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa, yace wannan hutu da gwamnati ta bayar takaitacce ne, ba hutu ne da dalibai zasu shantake a gida ba.

Ya kara da cewar baya ga jarabawar WAEC da ‘yan ajin karshe na Sakandire suka kammala, akwai kuma jarabawar NECO dake tafe da zarar an koma bakin aiki. Don haka wajibi ne daliban su koma a kan lokaci don tunkarar abinda ke gabansu.

Abdu Yalo ya yabawa Gwamnaatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusif, bisa kokarin da take na bunkasa harkar Ilimi a fadin Jihar, la’akari da irin ziyarce ziyarce da Gwamnan ke kaiwa Makarantu daban daban dake fadin Jihar, wanda hakan wasu alamu ne dake nuna shirin farfado da ingancin ilimi a fadin Jihar.

Kazalika Abdu Usman Yalo ya mika sakon Barka da Sallah Ga Gwamnatin kano da Masarautun Jihar Kano da kwamishinan Ilimi da Daraktocin Hukumar kula da Makarantun Sakandire da kuma Malaman Makarantun da sauran al’ummar Jihar Kano dama kasa baki daya.

Leave a Comment