Manyan Labarai

Ina Yabawa Jami’an Tsaron Katsina – Hon. Balele

Written by Pyramid FM Kano

Daga: KABIR GETSO

Dan Majalisar taraiya mai wakiltar yankin Dutsin-ma da Kurfi a majalisar Kasa, Hon. Aminu Balele (Dan Arewa) ne ya yi wannan kira a hirar sa da ‘yan Jaridu a ofishin sa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Ya ce a matsayin sa na Dan majalisar tarayya ya san irin kokarin da ake yi na tuntuba da tattaunawa da hukumomin tsaro domin lalubo hanyoyi da za su taimaka wajen ganin an kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da an cutar da su ba.

Hon. Balele, ya ce shi a karan kansa ya rubutawa dukkan jami’an tsaro  da suka hada da shugabannin ‘Yan Sanda da Civil Defence da sojoji da Jami’an tsaro na farin kaya da sauran su domin su kawo dauki wajen ganin an samar da tsaro da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Dan Majlisar ya yiwa  al’ummar yankin albishir  da cewa “nan bada dadewa ba komai zai koma kamar yadda yake a da na zaman lafiya da kwanciyar hankali”. In da ya ce manoma da ‘yan Kasuwa za su cigaba da harkokin su kamar yadda suka saba nan bada dadewa ba da ikon Allah.

Ya yabawa gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Radda game da irin jajircewa da yake yi na tabbatar da tsaro a Jihar ba dare ba rana; inda ya bukaci da ya cigaba da kokarin da ya ke yi har sai an sami ingantaccen tsaro da zaman lafiya a Jihar Katsina baki daya.

Leave a Comment