Labaran Jiha Siyasa

Ina Neman Afuwar Duk Wanda Na Batawa — Hafizu Kawu

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Kabiru Muhammad Getso

Dan majalisar Tarayya Mai wakiltar karamar hukumar Tarauni a Majalisar wakilai ta kasa Hafizu Kawu Tarauni ya Nemi Afuwar Duk wanda ya Batawa ko yayi masa laifi, bisa kuskure ko aka sami wani akasi.

Dan majalisar ya ce lokaci yayi da Al’umma zasu fahimci cancantar wanda ya kamata ya wakilcesu a Majalisar kasa.

Hafizu Kawu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai inda ya ce a tsawon shekarun da suka gabata ta wakilcinsa a Majalisa ya samar da ayyukan raya kasa daban daban a yankinsa da samawa matasa ayyukan yi da bangaren ilimi da koyar da sana’oi da bada jari.

Hafiz Kawu yace akwai wasu manyan ayyukan na nan tafe kafin karshen wa’adin sa musamman ga yankunan da ayyukan basu je gare su ba.

Ku Karanta: Zamu Tabbatar Da Karbo Kaso 13 cikin 100 Na Ma’adanan Da Ake Haka a Kano — Adamu Fanda

Hafizu Kawu yayi kira ga daukacin Al’ummar Tarauni da su sake bashi dama a zabe Mai zuwa inda zaici gaba da kawowa yankin kabakin arkizi.

Kazalika yaja hankalin matasa da su guji siyasar daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi,wanda hakan ke mai dasu baya wajen inganta cigaban rayuwarsu.

Ya kara da cewar duba da rawar da mata ke takawa a sha’anin zabuka hakan tasa yayi musu tsari na musamman da zai tallafi rayuwarsu tare da cigaba da samar masu da jari domin dogaro da kai.

Daganan Dan majalisar yayi addu’ar dorewar zaman lafiya a jihar kano dama kasa baki daya tare da neman afuwar duk wani wanda yake ganin an bata masa domin cigaban jam’iyyar APC a kakar zabe Mai zuwa.

Leave a Comment