Labaran Jiha

Hukumar Hisbah Tayi Holin Matuka Baburan Adai-daita Sahu Kimanin 100

Written by Admin

Daga: Jamila Suleiman Aliyu

Kimanin matuka Baburan a dai daita sahu guda 100 Hukumar Hisbah tayi holinsu a shalkwatarta da ke unguwar Sharada, wadan da suka taka dokar sana’ar daukan fasinja da ta aikin a kwaryar birnin Kano.

Da yake karin haske a kan matuka Baburan adaidaita sahun, Babban kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce, daga cikin an sami mutane 24 da laifin cakuda maza da mata a baburansu, sai mutane 35 wadan da suka yi askin banza, mutum 12 sun lika hotunan batsa a jikin baburansu, da wadan da ke sanye da gajerun wanduna mutum 11 da masu kure sautin kida ya yin tuki da sauransu.

Babban kwamandan Hisbah wanda ya yi magana ta hannun mataimakinsa mai kula da aiyukan yau da kullum (operations) Dr. Mujahid Aminudeen Abubakar yace, daga yanzu dakarunsa zasu ci gaba da sa ido domin tsaftace sana’ar adaidaita sahun a jihar Kano.

Babban kwamandan hukumar Hisbah yace, babban abin takaici, mafirinjaye daga cikin adadin wadan da dakarunsa suka kamo, ko da aka bukace su da gabatar da rukunan sallah ba su iya ba, daga ciki har da wadan da su ka kasa karanta Fatiha da sura dai.

Ya kara da shawartan iyaye da sauran jama’a da su dage wajen sauke nauyin da shari’a ta yi umarci uba ko uwa ya yi Musamman a kan neman ilimin addini da na zamani, dan samar da al’umma mai cike da tarbiyya da kyawawan aiki a rayuwa.

A karshe ya ba da umarnin ga sashin wayar da kai da na Da’awa da su koyawa wadan da su ka kasa karanta Fatiha da sura da wadan da su ka gaza kawo rukunan Sallah har sai sun iya a matsayin beli, tare da daukan cikakken suna da adireshi da lambar adaidaita sahun.

A nata jawabin mataimakiyar babban kwamandan Hisbah Mai kula da sashin mata, Dr. Khadija Sagir Sulaiman ta shawarci masu sana’ar tuka Baburan adaidaita sahun a jihar Kano da su ji tsoron Allah kuma su dai na cakuda maza da mata a baburansu domin samun daukaka da arziki a sana’ar.

Babban jami’in Hisbah Mai kula da sashin aiyukan yau da kullum, ACG Abubakar Salihu yace, Dakarunsa sun gabatar da sumame da cafke matuka Baburan na adaidaita sahun a kan titin gidan Murtala/BUK, da titin Kofar Kabuga/Kofar Ruwa, Kabuga/titin Tal’udu/zuwa Asibitin Murtala, da titin gidan Sarki/Kofar Nassarawa da sauransu.

Leave a Comment