Addini Da Dumi-Dumi

Hukumar Hisbah Ta Jinjinawa Naqeebatul Qadiriyya bBisa Kokarin Shirya Addu’o’i A Jihar Kano

Written by Pyramid FM Kano

Daga: JAMILA SULEIMAN ALIYU

Hukumar hisbah ta jihar Kano ta yabawa kungiyar mata musulmai sufaye bisa jajircewar ta akan harkokin ci gaban al’umma a jihar Kano. Mataimakiyar kwamandan hukumar a bangaren mata malama Khadija Sagir Sulaiman ce ta bayyana hakan yayin kaddamar da kungiyar tare da mauludin Sidi Abdulkadir Jilani R.T.A da kuma cikar Malama Baraka shekara goma akan kujerar Naqibatul Kadiriyya.

Dr. Khadija ta ce, fatan hukumar kungiyoyin su kasance manyan ayyukansu sune hidimtawa addini domin babu dacen da yakai haka, don haka ta ja hankalin kungiyar mata musulmai sufayen da su kaucewa son zuciya ko neman biyan bukatu na kashin kansu ba tare da sun fifita harkar musulumci a sahun gaba ba.

Malama Baraka Adamu Danfanta ta nuna jin dadinta game da kaddamar da kungiyar tare da kasancewar ta a matsayin Naqibatul Kadiriyya a jihar Kano. Naqibatul Kadiriyyar ta kuma yi fatan dukkan addu’o’i’n da akayi a wannan wuri su zama karbabbu.

Taron ya samu halattar manyan baki kamar jigo a jam’iyyar APC wanda ya wakilci gwamna Honorabil Sunusi Surajo Kwankwaso da kuma Galadiman Gado da Masun Kano Alhaji Dayyab Ahmad Mai Turare da sauransu.

Daga Karshen, an gudanar da addu’o’i’n samun sassauci da kunci a rayuwar musulmai baki daya.

Leave a Comment