Addini

Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Kuduri Aniyar Tallafawa Kungiyoyin Mata Don Tsara Al’amuransu Daidai Da Addini

Written by Pyramid FM Kano

Daga: JAMILA SULEIMAN ALIYU

Hukumar hisbah ta jihar Kano ta ja hankalin kungiyoyin mata da suke rajin kare haqqin mata da yara dasu kaucewa bin diddigin laifukan maza da nufin kawo karshen cin zarafin mata da yara.

Mataimakiyar kwamandan hukumar a bangaren mata Dr. Khadija Sagir Suleiman ce tayi wannan kiran a yayin ziyarar da kungiyar kare haqqin mata da yara ta Baubab ta kawo musu ziyara ofishin hukumar hisbah dake Sharada a inda tace, muddin kungiyar ta na son a fahimci manufarta to babu shakka sai ta kiyaye da fifita mata akan maza domin a zauna lafiya sannan su fi bayar da karfi wajen ganin matan sun gyara dabi’unsu kamar yadda mahalicci yace mata da mazan suyi mu’amala da kyautatawa a tsakaninsu.

Itama a nata bangaren shugabar kungiyar kare haqqin mata da yara ta Boubab Hajiya Zubaidah Ahmad Nagi, tace, sun kawo ziyarar ne domin neman goyon bayan hukumar hisbah ta fuskar kawo karshen cin zarafin mata da yara da wasu daidaikun maza kanyi tare da bayyana irin ayyukan da sukeyi domin tallafawa rayuwar mata da yara. Dr. Khadija Sagir Suleiman ta kara jaddada musu dasu bawa gyaran tarbiyyar matan fifiko.

Leave a Comment