Labaran Kasa

Hukumar Hana Fasakwauri Ta Kama Kayayyakin Da Doka Ta Tana Shigowa Da Su Kasar Nan

Written by Admin

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu 

Hukumar Hana fasakwauri ta kasa shiyyar kaduna ta yi alwashin cigaba da dakile shigowa da kayayyakin da doka ta hana zuwa kasar nan.

Jami’in hukumar mai kula da shiyyar a kaduna wato zone B Comptroller Dalha Wada Chedi ya sanar da haka yayin Taron manema Labarai dangane da ayyukan hukumar a shiyyar watan Fabrairu zuwa karshen wannan wata na Maris da muke ciki.

Ya ce a tsakanin wannan lokaci hukumar ta samu nasarar kama kayayyaki daban-daban na miliyoyin Naira da aka shigo da su kasar nan ba bisa ka’ida ba.

Comptroller Dalha Wada Chedi ya ce jami’an hukumar na aiki babu dare babu rana wajen cigaba da aiki wajen dakile shigowa da kayayyakin da basa bisa doka kasar nan musamman a wannan lokaci da kungiyar ECOWAS ta bakin Shugaban kasa Bola Tinibu ya bayar da umarnin bude iyakokin Nigeria da Mokobtan ta musamman Jamhuriyar Niger.

Ya Kuma Kara Jan hankalin Al’uma da su kauce wa wannan dabi’a ta shigowa da kayayyakin da basa bisa doka kasar nan kasancewar akwai doka da ka’idoji da aka Samar da suka kamata kowa ya bi idan yana bukatar shigowa ko Kuma fitar da kaya kasar nan.

Comptroller Dalha Wada Chedi ya Kuma yaba wa sauran Jami’an tsaro bisa yadda suke tallafawa hukumar domin samun nasarar ayyukan ta.

Leave a Comment