Labaran Jiha Muhalli

Hukumar Hadeja-Jama’are Ta Karyata Rahotannin Ballewar Dam Din Tiga

Written by Pyramid FM Kano

Hukumar raya kogunan Hadeja Jama’are tana amfani da babbar murya wajen karyata wasu hotanni da hotuna da ake yadawa cewa dam din Tiga dake karamar hukumar Bebeji a Jihar Kano ya Balle.

Shugaban Sashen Hulda da jama’a na hukumar Kuma sakataren harkokin Mulki Salisu Baba Hamza ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a nan Kano.

Sanarwar ta ce tun farkon watan Agusta ruwan kogin ya fara fita kuma har yanzu ruwan Yana cigaba da fita ta hanyar da aka tsara masa ya fita domin rage yawansa.

Hukumar ta ce sakamakon mamakon ruwan sama a jahohin Kaduna da Plato dam din ya kara tumbatsa kuma fitar ruwan ta karu daga kogin.

Salisu Baba ya Kara da cewa “kar a manta wannan lokaci ne na damuna kuma muna cikin watanni da ake samun mamakon ruwan sama sannan dama hukumar kula da yanayi ta Najeriya tayi hasashen fuskantar ruwa da yawa a sassan wannan kasa”.

Ku karanta: Muna Rokon Gwamnatin Kano ta Gyara Titin Railway zuwa Audu Bako — Mamuda Zango-Kabo

Kogunan dake karkashin hukumar raya kogunan Hadeja Jama’are basu taba samun kulawa kamar a irin wannan lokaci ba musamman bayan kammala ayyukan gyara madatsun ruwa domin inganta Noman rani na TRIMMING hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar ruwa ta Tarayya da bankin duniya.

“Wannan hukumar ta Hadeja Jama’are tana kira ga masu makwaftaka da kogin su rika bada rahoton duk wani bakon abu da suka gani a dam din na Tiga yayinda hukumar ke bada tabbacin aminci da kariya daga tsarin kulawa da kogin”.

Leave a Comment