Addini

HUDUBA: Ku Guji Shirka Da Hana Zakka Da Karbar Rashawa — Limamin Masallacin Dangi

Written by Pyramid FM Kano

Limamin Masallacin Umar Bin-kattab dake kan titin zuwa Zaria a cikin kwaryar birnin Kano Dakta Yahaya Tanko ya ja hankalin Al’ummar Nigeria musamman musulmi da su guji yin Shirka da Hana Zakka gami da Karba ko bayar da Rashawa don gudun fushin Allah.

Dakta Yahaya Tanko ya bayyana hakan ne cikin hudubar sallar Jumaa da ya jagoranta a baya-bayan nan a Kano.

Ya ce matukar al’umma za su rika hada Allah da wanin sa babu makawa sai sun fuskanci fushin sa, kuma babu komai a ciki sai wahala da Talauci da zaba kala-kala.

“Matukar mutane zasu rika bautawa wani ba Allah ba, matukar mutane zasu rika daukar wani zai azurtaka ba Allah ba, akwai Mai kashewa ko rayawa ba Allah ba, matukar mutane zasu rika daukar wani zai yaye Maka wata matsala ba Allah ba, to lallai wannan Shirka ne”, inji Tanko.

Ku Karanta: Madrasatul Ihya’us Sunna Littahafizul Qur’an Ta Yi Sauka Al’qur’ani Da Walima Na Dalibai 13 a Bagwai

Malamin ya kuma bukaci al’umma Musamman madawata da Gwamnatoci da Yan kasuwa da su rika fitar da hakkin Allah a dukiyar su (Zakka), yana mai cewa hakan yana tsarkake dukiyar da Kara yalwarta.

Dakta Tanko ya cigaba da cewa dukkan matsalolin da Nigeria ke fuskanta na tabarbarewar tsaro da hauhawar farashin kayan masa rufi sun samo asali ne daga abubuwan da cin hanci da Karbar Rashawa ke haifarwa, yana mai cewar idan ana son saituwar komai dole sai an yaki cin hanci da Rashawa da kuma saka komai a gurbinsa.

Ku Karanta:Kulawar Iyaye ce Hanyar karfafa Gwiwar Malamai Don Bada Ingantaccen Ilimi — Hafizu Garko

A cewarsa malamin Karbar Kudin ruwa a cikin bashi ya sabawa koyarwar addinin musulunci kuma zalunci ne karbar Kudaden wanda babu abun da suke haifarwa wanda ya Karba walau dai-daikun mutane ko rukuni ko Gwamnatoci sai musifa, yana mai cewa karbar bashi ya halarta a musulunci Amma a saka ruwa ko Kari akan abun da aka Karba ya sabawa addinn musulunci domin Allah yayi hani da hakan cikin littafinsa Mai zarki (Alqur’ani).

Daga nan Limamin Masallacin na Umar Bin-kattab ya koka kan irin bashin da ake bin Nigeria, inda ya Kara da cewa matukar za’a cigaban da Karbar bashi tattalin arzikin Nigeria zai cigaba da samun targaro.

Leave a Comment