Addini

HISBAH: Za Mu Yi Aiki Kafada-da-Kafada Da Takwarar Mu Ta Kaduna Don Cigaban Musulunci — Ibn Sina

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Jamila Suleiman Aliyu

Hukumar hisbah ta jihar Kano ta ce zata cigaba da aiki da Takwararta ta jihar Kaduna domin Dabbaka harkokin Addinin Musulunci.

Shugabar Hukumar na jihar Kano Dakta Haroon Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan a ziyarar aiki da ya kaiwa takwaransa a Kaduna.

Haroon Ibn Sina wanda mataimakinsa a bangaren horarwa Malam Idris ibn Umar ya wakilta ya ce babbar nasara ce da hukumar a jihar Kaduna ta samar da Dakarunta a Zaria da kewaye domin zai tallafa wajen yaki da Badala da kuma aikata Bai dai-dai ba a jihar.

Ku Karanta: Mun Horar Da Matasa 350 Gyaran Waya A Shekara Daya — Shugaban “Huzy Comms”

Malam ibn Umar ya ce adadin sababbin dakarun su 75 a zazzau zai taimakawa hukumar kwarai da gaske wajen gudanar da ayyukan ta.

Ibn Umar ya ce Kofar hukumar Hisbah ta jihar Kano a Bude yake wajen Neman shawara da goyon baya ko horarwa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Leave a Comment