Addini Labaran Jiha

Hisbah Da MULAN Sun Hada Hannu Domin Kare Ayyukan Hukumar A Kano

Written by Admin

Hukumar Hisbah da Kungar Lauyoyi Musulmi ( MULAN) ta kasa, reshen jihar kano sun yi alkawarin hada hannu domin kare aiyukan hukumar da kuma samar da dai daito a tsakanin jama’a, Musaman a kan bin dokokin shari’ar musulunci da bin tsarin aiwatar da aiki bisa ka ida.

Babban kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shine ya sanar da hakan a tattaunanawa ta Musaman da tawagar mambobin kungiyar a lokacin da su ka ziyarci shalkwatan hukumar da ke unguwar Sharada, domin gabatar da kansu ga hukumar a matsayinsu na sabbin shugabannin kungiyar a jihar Kano.

Babban kwamandan wanda ya sami wakilcin, Babban Daraktan hukumar (DG), Alhaji Abba Sa’id Sufi ya ce, tabbas Hisbah a jihar Kano na bukata tare da farin cikin yin aiki da ya ya kungiyar Lauyoyi Musulmi duba da yawan tarin korafi da aiyukan sulhu masu tarin yawa da hukumar kan samu daga jama’ar, Najeriya masu bin addinai da ban da ban.

Ya kara da cewar, hukumar Hisbah na bukatan hada hannu dan gudar da bita a kan kare hakkin jama’a a karkashin dokar kasa tare da illimantar da Dakarunsa hakin da ya rataya a kan su dan gudun wuce gona da iri, da ciyar da Dakarunsa dabarun gudanar da sulhu a tsakanin ma su korafi a zamanance.

Ya ce, a shekarun baya, kungiyar Lauyoyi Musulmai, da wasu daga cikin ya yanta sun bawa hukumar Hisbah gudun mawa ta fuskar shari’u a kotuna, ciki har da gudunmawar gudanar da aiki kyauta ga hukumar wanda hakan ya taimaka matuka gaya ga jama’ar jihar Kano, ba tare da daukan dogon lokacin ba, wanda hakan ya rage cinkoso a kotunan musulunci.

Babban kwamandan, ya yi alkawarin bawa ‘ya’yan kungiyar aiki har da basu alawus a duk karshen wata, matukar sun bukaci haka tare da barin kofa a bude a kowanne lokaci dan karban gyara ko shawaran gyara aiki mai ma’ana ga jama’a da hukumar kanta.

Tun da fari a jawabin Shugaban kungiyar Lauyoyi Musulmi (MULAN) reshen jihar kano, Bar. Sunusi Lawan Fandubu yace sun ziyarci hukumar Hisbah ne dan gabatar da kansu a matsayinsu na sabbin shabanin kungiyar, tare da tattauna mahimman batuwa wadan da za su ciyar da aikin Hisbah ga ba, da dai dai ta aikin Hisbah izuwa na zamani.

Barr. Sunusi Lawan Fandubu, ya yi magana da kakkausan harshe cewar daga yanzu shagabancin kungiyar Lauyoyi Musulmi ta jihar kano ta dai na sa ido wasu mutane na cin zarafin hukumar, a wasu lokutan har da cin mutuncin Dakarunta, tare da shan, alwashin kungiyar zata yi dukkan mai yuwa dan bawa hukumar kariyan da takamata a dukkan matakan shari’a ko Ina kuma a kowanne lokaci, mutukar bukatar hakan ta ta so.

Ya kara da cewar, kungiyar Lauyoyi Musulmi ta jihar kano za ta yi amfani da damanta domin magance satar yara daga jihar kano izuwa wasu jihohin, inda ta bukaci hukumar Hisbah da ta bude ofis a addukan tashoshin mota dan jami’inta su kara sa ido.

 

Leave a Comment