Ilimi Labaran Jiha

Hanyoyin Da Kano Zata Inganta Dangantakar Ta Da Canada

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin Jihar Kano zata karfafa dangantaka da kasar Canada ta fuskar ilimi da kiwon lafiya.

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Canada James Christopher a ofishinsa.

Ya godewa jakadan kasar Canada bisa tallafin da kasarsa take bawa al’umar jihar Kano a bangaren noman rani da yaki da zaizayar kasa da kwararowar hamada.

Leave a Comment