Addini Labaran Jiha Manyan Labarai

Dalilin da ya sa Gwamna Ganduje bai Zartar da hukuncin kisa ba ga wadanda suka kashe Hanifa

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Mustapha Gambo Muhammad

Gwamnatin jihar Kano ta sake tabbatar da kudirinta na kammala cika dukkanin ka’idojin Shari’a da suka kamata tare da sanya hannu domin zartar da hukuncin kisa da aka yankewa Abdulmalik Tanko da Hashimu Isiyaku wadanda kotu ta samu da laifin kashe Hanifa Abubakar dalibar Yar shekara 5.

A ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata ne Jostis Usman Naabba na babbar kotun Jihar Kano ya sami wanda ake tuhuma na farko da na biyu da laifin Hadin Baki Garkuwa da dalibar gami da kashe ta tare da binne gawar ta, lamarin da ya sa alkalin ya yankewa dukkan mutane biyun hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya gamsu da hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar a gabansa.

Bayan hukuncin kisa, kotun ta Kuma yanke musu hukuncin zaman gidan gyaran hali na wa,adin shekaru 5 ga Abdulmalik Tanko da kuma 4 ga Hashimu Isiyaku bayan samun su da laifi a wasu tuhume-tuhume uku da aka yi musu, yayin da kuma kotun ta yankewa mutum na uku da ake tuhuma a shari’ar wato Fatima Musa wacce kotun ita Kuma ta yanke mata zaman shekaru biyu a gidan gyaran hali.

Tun a lokacin da ake shara’ar Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yayi alwashin sanya hanu akan hukuncin kisa matukar kotu ta yanke musu hukuncin, to Amma shara’ar wacce aka kammala a cikin abin da bai wuce watanni 6 ba, yanzu ta fara janyo kace nace kan ko gwaman zai saka hanu akan hukuncin kisan ko akasin hakan, harma wasu na ganin zaa iya barin wanda suka aikata mummunan laifin su ta fi ba tare da an dauki mataki a kansu ba.

Da yake bayani dangane da batun, kwamishinan sharia na jihar Kano Barista Musa Abdullahi Lawan yayi watsi da ce-ce-ku-cen da ake yi, inda ya bada tabbacin cewa Ganduje zai sanya hannu domin zartar da hukuncin kisan.

Ku Karanta: Kotu Ta Ki Amincewa A Mayar Da Shari’ar Abduljabbar Abuja

Ya ce duk da cewa hukumar kula da gyaran Hali ta kasa ce ke da alhakin bada takardar sanya hannu, amma hakan zai tabbata ne idan lokacin daukaka kara na kwanaki 90 ya wuce.

Musa Abdullahi Lawan ya ce wadanda aka yankewa hukuncin har yanzu suna da damar daukaka kara.

Kwamishinan ya Kuma yabawa Alkalin kotun da ya saurari karar tare da yanke hukuncin ba tare da Jan dogon lokaci ba a Shari’ar.

Leave a Comment