Kasuwanci

Hana ‘Yan China Kasuwanci a jihar Kano Shine Zai Habbaka Kasuwancin Jihar

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Gamayyar kungiyoyin ‘yan kasuwar kasar nan reshen Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta hana ‘yan kasar Sin (China) shigowa kasuwannin kasar nan domin gudanar da harkokin kasuwancin.

Kiran ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar gamayyar ‘yan kasuwar kasar nan reshan Jihar Kano Alhaji Auwal Mallam Iliyasu yayin zantawa da manema labarai. Inda Alh. Malam ya kara da cewa ya zama dole gwamnati tasa doka wajen harkokin kasuwancin Kano musamman Yan kasar china masu shigowa suna bata farashin kaya.

Ya kara da cewar ‘yan kasar Sin na kawo tarnaki da koma baya musamman wajen farashin kaya.

Leave a Comment