Da Dumi-Dumi

HADA HANNU GURI GUDA SHINE ZAI HABBAKA KASUWANCI A KANO

Written by Pyramid FM Kano

By: ADAMU DABO

An yo kira ga ‘yan kasuwa dake fadin jihar Kano da su hada hannu guri guda domin habbaka harkoki da bunkasa kasuwanci a fadin jihar Kano.

Kiran ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin kula da kasuwar kofar wambai Alhaji Nasihu Ahmad Garba Wanda aka fi Sani da wali Dan China ya yin zan tawa da manema labarai.

Wali Dan China ya ce ya zama wajibi gwamnati da sauran masu hannu da shuni su taimaka wajen habbaka kasuwanci a Jihar Kano.

Haka zalika ya Kara da cewar akwai sabbin tsare tsare da ya kawo a matsayinsa na Saban shigaba domin inganta harkokin kasuwancin kasuwar kofar wambai.

Ya Kuma Yi kira ga jami’an tsaro da su hada hannu guri guda domin habbaka harkokin tsaro a fadin kasuwar ta kofar wambai.

Leave a Comment