Labaran Jiha

Gwamnatin tarayya ta kalli masu kananan sana,oi akan cire tallafin man fetur.

By: IBRAHIM SANI GAMA

Kungiyar kasuwar masu sana’ar magunguna ta Jihar Kano dake malam Kato ta yi kira ga al’ummar Najeriya, da su kwantar da hankulansu sakamakon tashin gwauron Zabi da man fetur yayi saboda cire tallafin mai da Gwamnatin tarayya tayi.

Shugaban kula da al’amuran da suka shafi matasa, Alh. Mamuda Zangon Kabo ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa dake Kasuwar.

Mamuda Zangon Kabo yace, kamata yayi al’ummar Najeriya su ci gaba da gudanar da addu’o’in samun sauki daga wajen Allah subhanahu wata’ala, kasancewar itace kawai mafita ga ‘yan Najeriya.

Ya kuma, bukaci Gwamnatin tarayya da ta tausayawa al’ummar kasar nan, musamman wadanda basu da hali, kuma ba ma’aikatan Gwamnati bane, duk da cewa Gwamnatin tarayya tana cewa za ta karawa ma’aikatanta Albashi.

Shugaban ya bayyana cewa, su kansu al’ummar Najeriya abin a duba lamarin sune saboda halin matsin rayuwa da za su tsinci kansu, da yawa wasu daga cikin al’umma sai sun fita za su samu abin da za su ciyar da iyalansu wadanda akasari sune suka ci yawa a fadin kasar nan.

Mamuda yace, akwai kananan ‘yan kasuwa da suke da karancin jari da za su gudanar da sana’o’insu na yau da kullum, amma cire tallafin da Gwamnatin tarayya tayi, ya kara durkusar da su, sakamakon tashin kayayyakin masarufi, duba da man fetur yana tafiya kowanne fannin na rayuwar al’ummar Najeriya.

Haka zalika, Zangon Kabo, ya shawarci masu kananan sana’o’i da ‘yan kasuwa da su kasance masu yin lissafi a kasuwancinsu na yau da kullum domin fahimtar yadda kasuwancinsu yake tafiya, Wanda yin hakan zai taimaka musu wajen sanin inda suka dosa.

Daga karshe ya shawarci kungiyoyin ‘yan kasuwa da manyan ‘yan kasuwa da su kasance masu tallafawa kananan ‘yan kasuwa da suke da karancin jari domin tallafa musu a harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.

Leave a Comment