Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Kano Zata Sa Ido Akan Masu Ta’adar Yin bayan Gida A Kasa – RUWASSA

Daga: KABIR.GETSO

Shugaban Hukumar samar da ruwa a karkara da tsaftace shi na jihar Kano wato (Rural Water Supply and Sanitation Agency, RUWASSA) Engr. Shawilu Abdukadir Isah ya bayyanna kokarin da Gwamnatin Kano ke yi don samar da dabarun samar da ruwa a yankunan karkara da kuma tsaftace shi.

Engr. Shawilu ya bayyanna hakan ne a taron manema labarai da ya gudana a harabar hukumar a yau Litinin, yace babu shakka sha’ainin samar da Ruwa da tsaftace shi abu ne mai matukar mahimmanci ga rayuwar al’umma, wannan yasa Gamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ta himmatu wajen cigaban tsarin.

Shirin zai maida hankali akan magance yin bayan gida barkatai musamman a yankin karkara inda hakan ke ta’azzara gubacewar ruwa, da haifar da cututtuka, don haka Hukumar ta shirya tsaf domin fara gudanar da bita ta musamman a gundumomi daban daban dake fadin jihar Kano, inda tuni shiri yayi nisa wajen farawa da kananan Hukumomi 8 dake Jihar ta Kano.

Engr. Shawilu ya Kuma bayyanna wasu sabbin tsare tsare da Hukumar ta RUWASSA tayi shiri domin cigaban Jihar kano baki daya. Daga cikinsu akwai gyaran kayayyakin samar da ruwa dake Hukumar da kuma farfado da hanyoyin samar da ruwan sha sai kuma batun samar da sabbin kayayyakin samar da ruwan sha da tsaftace shi da kuma shirin wayar da kai don tsaftace muhalli a dukkanin garuruwa.

Shugaban Hukumar Engr. Shawilu Abdukadir ya ja hankalin al’umma da su guji saurin yada wasu bayanai a kafafen sada zumunta akan abinda ya shafi tsaftar ruwan sha a wasu yankunan, maimakom hakan kamata yayi a tura da korafi kai tsaye a dukkanin Ofishin Hukumar dake kananan Hukumomin jihar ta Kano.

Engr. Shawilu ya godewa al’ummar jihar Kano bisa irin gudummuwar da ake bawa Gwamnatin kano don samun nasarar ayyukan da take gudanarwa yau da kullum.

Leave a Comment