Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Kano zata bada kulawa ta musamman ga ‘Yan Fansho

By: KABIR GETSO

Hakan ya fito daga shugaban hukumar pension Alh Habu Mohd Fagge a lokacin da ya kai ziyara ofishin kungiyar ‘yan fansho tare da kadarorin ‘Yan Fanshon dake kan titin Panshekara da gidajen Kwankwasiyya da Amana. Shugaban hukumar Fanshon Alh Habu Mohd Fagge ne ya kara da cewar Hukumar tayi shiri sosai don ganin an samu canji da Yakama ga ‘yan Fansho.

A nasa jawaban shugaban kungiyar ta jihar Kwamared Salisu Ahmed Gwale ya jinjinawa gwamnan Kano bisa kawo shugaban mai nagarta mai kuma tausayawa ‘Yan Fansho tare da Alkawarin bashi goyan baya dari bisa dari.

Kazalika, kananan ma’aikatan hukumar fansho sun gudanar da addu’o’i na musamman ga sabon shugaban hukumar Alh Habu Mohd Fagge da nufin Allah yayi masa jagoranci.

Sun Kuma yabawa sabon Gwamnan saboda kawo ma’aikaci mai kula da rayuwa ma’aikata.

Babban sakataran dindin na hukumar ta Fansho Alh Yahaya Nuhu Danbatta ya bukaci M’aikatan dasu kula da Zuwa aiki  da wuri da bin dokokkin Gwamnati.

Leave a Comment