Labaran Kasa Muhalli

Gwamnatin Kano Za ta Nemi Tallafin Bankin Duniya Don Gina Dam-dam Uku

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana neman Bankin Duniya da sauran abokan huldar ci gaban kasa-da-kasa da su yi Aikin Hadin Gwiwa domin Gina Dam-Dam guda uku da kula da wuraren da zaizayar kasa guda biyar (5) a kananan hukumomi takwas (8) a nan Kano da nufin yaki da kwararowar Hamada.

Gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje (OFR) ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagorancin bikin bude aiwatar da aikin yaki da matsalolin da canjin yana Kai haifar Wanda aikin Hadin Gwiwa ne tsakanin Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya ta hanun ma’aikatar Gona da ma’aikatar Samar da ruwan sha da wanda kuma za’a gudanar da shi a jihohin Arewacin kasar nan 19 da ma Babban birnin Tarayya Abuja.

Dakta Ganduje wanda sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ya wakilta ya ce jihar ta gabatar da wasu wurare tara (9) ga bankin duniya wadanda suka hada da wuraren da zaizayar kasa guda biyar da kuma guraren kula da gine-ginen madatsun ruwa guda hudu (4).

Ya ce, “Duk da cewa jihar ta samu takardar izini na tsarin kula da madatsun ruwa guda daya (1) kacal a ‘Yan Sabo da ke karamar hukumar Tofa wanda aka kammala kashi 100 bisa 100. “Haka Kuma an kammala zanen sauran gine-ginen kula da ruwa guda uku (3), na farko a Dambazau cikin Karamar hukumar Takai da Dawan Kaya a Makoda da ‘Yartiti a Shanono. Hakazalika, an samu guraren biyar da matsalar zaizayar kasa ta shafa a garin Rarin cikin Karamar hukumar Dawakin Tofa da Bulbula-Gayawa a Nasarawa da Tudun-fulani a Ungogo da Unguwar Alu a Tarauni da Kamanda a cikin karamar Kiru. “Duk muna neman tallafin Bankin domin aiwatar da su a karkashin Shirin ACReSAL”.

Ku karanta: Allah Ya Isa Ga Masu Zuba Mana Shara A Tsakiyar Titin Kabara — Kabiru Getso

A nasa jawabin, kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bayyana kudirin gwamnatin jihar na inganta da kare muhalli inda ya ce jihar ta dawo da aikin dashen bishiyu na shekara-shekara ta 2020 da nufin kare Kano daga illolin da sauyin yanayi ke haifarwa.

Dakta Getso ya ce jihar ta ba da fifiko ga bangaren muhalli ta hanyar magance matsalolin yanayi da maido da gurbatacciyar kasa da yaki da matsalar kwararowar hamada da kawar da gurbacewar muhalli da tsaftace muhalli da kuma rigakafin ambaliya da shawo kan matsalar.

Ya ce wasu daga cikin ayyuka da kuma shirye-shiryen sun hada da “kafa hukumar kula da gandun daji ta jihar Kano da kuma dasa itatuwa da nufin kara yawan itatuwa da kuma kula da dazuzzuka a jihar”.

“Gwamnatin jihar Kano tana ta shiga wani tsari na Gwamnatin Tarayya domin inganta samar da bishiyoyi da samar da kudade da filaye ko kafa cibiyoyin kula da bishiyoyi da gonakin al’umma a jihar,” inji shi.

Getso ya kara da cewa, “Mun ci gaba da gudanar da aikin share magudanan ruwa na shekara-shekara domin dakile ambaliyar ruwa a jihar inda a shekarar 2022 da muke ciki muka yashe magudanan ruwa da yawansu ya Kai mita dubu 70 a kwaryar birnin Kano”.

Ku karanta: Cushe Magudanan Ruwa Ke Jawo Ambaliya — Dan-azumi Gwarzo

Ita ma da take nata jawabin, shugabar ayarin bankin duniya Dr Joy Iganya Agene ta yaba da kokarin da kuma jajircewar gwamnatin jihar Kano wajen daukar nauyin shirin, inda ta kara da cewa shirin na sama da dala miliyan 700 ya mayar da hankali wajen magance illolin sauyin yanayi a Arewacin Najeriya.

Ta ce tawagar za ta yi kokarin ziyartar wuraren da abin ya shafa domin ganin wuraren da ke bukatar tuntubar da wuri da kuma wadanda ke bukatar tsattsauran shiri don inganta aikin.

Taron ya samu halartar kwamishinan noma da raya karkara na jihar Kano Yusuf Jibrin Rurum da kwamishinan albarkatun ruwa na Kano Garba Yusuf Abubakar wanda ya samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar Hussain Umar Ganduje, da wakilai daga ma’aikatar muhalli ta Tarayya, da Ma’aikatar noma da albarkatun ruwa ta tarayya da wakilan jihohin arewacin Nigeria 19 da kuma ‘yan jaridu.

Leave a Comment