Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Kano Ta Yabawa Shirin Na AGILE

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Shirin nan na tallafawa ‘yan mata domin inganta harkokin iliminsu a makarantu Wanda a turance ake cewa adolescent girls initiative for leaning and empowerment (AGILE).

Yaban ya fitone daga kwamishinan ilimi na Jihar Kano wanda babban darakta dake ma’aikatan ilimi mai kula da harkokin hadin gwuiwa kungiyoyi da ma’aikatar ilimi Malam Salisu Idris ya wakilta a yayin wani taro da shirin na AGILE ya shirts a karamar hukumar Kabo domin wayar da Kai ga iyaye da ‘yan mata akan muhimmancin ilimin ‘ya mace ga al’ummah.

Idris ya Kuma yabawa yadda shirin ke kara-kaina wajen ganin yara mata sun koma makarantu domin sumun ilimin zamani.

Shima a nasa jawabin jigo a cikin shirin Dr. Auwal Halilu yace duk lokacin da ‘ya mace da samu ilimi dole ta bambanta da wace bata da shi.

Dr. Hauwa Muhammad Gimba Malam ce a Jami’ar Bayero ta bayyana muhimmancin ilimi ga ‘ya mace a cikin Alumma ayau musamman yanayin da duniya ke ciki a yau.

Barr. A’isha Ismail malamace a Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies ta bayyana cewar duk wata daukaka bata yiyuwa sai da ilimi na addini da na zamani saboda haka wajibine ‘ya mace ta nemi ilimi.

Daga karshe Haj. Abu Umar ita ce mai kula da harkokin wayar da kai na shirin AGILE ta ce shirin na tallafawane wajen bayar da dukkanin abubuwa da ‘ya mace ke bukata wajen samar da ilimi addini da na zamani ga ‘ya mace domin ta dogara da kanta.

Taron shirin na AGILE ya samu halartar mutane da dama kama daga iyaye maza da mata masu rike da madafan iko a karamar hukumar Kabo.

Leave a Comment