Muhalli

Gwamnatin Kano Ta sha Alwashin Kawar Da Dukkan Sharar Dake Fadin Jihar Nan

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin Jihar Kano ta samar da sabbin motocin kwashe shara guda goma da zata yi amfani da su wajen kwashe tudun sharar dake fadin jihar.

Shugaban hukumar kwashe shara na Jihar Kano Alhaji Haruna Danzago ne ya sanar da hakan a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan Kano.

Shugaban ya bayyana cewar daga cikin ayyukan hukumar akwai kwashe shara da tsaftar muhalli da kuma feshin maganin sauro.

Ya kuma bayyana cewar farkon kama aikinsa a hukumar ya tarar da mota daya ce kawai take aiki wanda yanzu sun gyara 7 daga ciki, sai kuma wanda shugaban hukumar karbar korafe korafe na jihar Barista Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya karbo guda takwas da aka yi gwanjonsu ba bisa ka’ida ba.

Kazalika, ya ce babura masu kafa uku da ake kwashe shara guda daya ne kawai yake aiki wanda sun fi dari a hukumar, amma daga zuwansu sun gyara sama da guda goma sha biyar.

Alhaji Danzago ya kara da cewa a kullum ta Allah tun daga fara aikinsa a hukumar suna yin sawu arba’in wani lokacin ma har sau saba’in na kwashe tudun sharar dake fadin jihar.

Daga nan kuma, sai ya yi kira ga kungiyoyin aikin gayya kan cewar duk lokacin da zasu yi aikin gayya su tabbata sun sanar da hukumar su domin ta turo jami’anta su kwashe sharar da suka tara.

Leave a Comment