Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Kano Ta Sha Alwashin Cigaba Da Aikin Titunan Kananan Hukumomi 44 Dake Kano – Kwamishinan Ayyuka

 

Daga: KABIR GETSO

Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na jihar Kano Engr. Marwan Ahmad ya shaidawa manema labarai cewa tuni shirin Gwamnatin Kano yayi nisa na bawa ‘yan Kwangila dama don cigaba da ayyukan titunann kananan hukumomi 44 dake Kano.

Ya bayyanna hakan ne a yayin rangadin duba yadda aikin ke gudana a kananan hukumomin Gezawa da kuma Albasu a ranar Asabar din da ta gabata.

Yace abin takaici ne ganin yadda Gwamnatin baya tayi watsi da irin wannan ayyuka duba da mahimmanci su ga rayuwar al’umma, musamman na yankin karkara inda aka barsu a baya wajen samar da ingantattun hanyoyin sufuri.

Kwamishinan yayi kira ga ‘yan kwangila da su jajirce domin cigaba da aikin cikin inganci kamar yadda tsarin aikin yake tun a baya, “wannan Gwamnatin ta shirya tsab don bawa ‘yan kwangila hakkokinsu domin tabbatar da cigaban aikin yadda ya kamata inji Kwamishinan “.

Wasu daga cikin mazauna yankin na Gezawa da Albasu sun bayyanna farin cikinsu ganin yadda aikin ya dawo gadan gadan, inda suka yi kira ga ‘yan kwangilar su rike amanar da aka basu na yin aikin da ya dace duba da irin wahalar da suke fuskanta Musamman a wannan yanayin na damuna da ake ciki a sakamakon rashin aikin hanyar.

A Zantawarmu da ‘yan Kwangilar sun tabbatar da cewa zasuyi aiki tukuru mai inganci don sauke amanar da aka basu,inda suka yabawa Gwamnaatin Jihar Kano bisa wannan kokari na dawo da cigaban wannan aiki, wanda ya kwashe shekaru ba’a kammala shi ba.

Engr. Ahmad ya roki al’ummar yankin da su bada cikakken hadin kai don samun ingantattun ayyukan a yankin nasu, Musamman ta fuskar dakatar da zuba shara barkatai a magudanan ruwa da sauran Abubuwan da zasu kawo cikas ga aiki.

Engr. Marwan yabawa Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf bisa wannan namijin kokari inda ya shaidawa al’ummar Jihar nan bada dadewa ba za’a kammala dukkan wadannan ayyuka, domin tuni Gamnatin ta ware makudan kudade don cigaban ayyukan.

Leave a Comment