Lafiya

Gwamnatin Kano Ta Kashe Sama Da Miliyan 15 Don Siyan Kayan Tallafawa Masu Juna Biyu Da Wadanda Suka Yi Hatsari

Written by Pyramid FM Kano

Daga: Muktar Yahaya Shehu

Gwamnatin jihar Kano ta kashe sama da naira miliyan 15 domin Siyan kayayyakin tallafawa mata masu juna biyu da kananan yara gami da wadanda suka hadu da ibtila’in Hatsari a titinan jihar.

Shugaban hukumar kula da manyan asibitoci ta jihar Kano Dakta Nasiru Alhassan Kabo ne ya sanar da haka yayin kaddamar da rabon kayayyakin karon Farko a shekarar 2023.

Ya ce gwamnatin jihar na samar da kayayyakin a duk wata domin rarraba su a dukkanin manya da kananan asibitocin jiha a kokarin da ake na tallafawa sha’anin Kula da lafiyar kananan yara da kawo karshen matsalar mace-macen mata yayin haihuwa.

Dakta Kabo wanda Daraktan kula da lafiya na hukumar Dakta Sulaiman Hamza Mudi ya wakilta ya ce a babban asibtin kwararru na Murtala kadai a Shekarar da ta gabata mata dubu 15 da 577 ne suka haihu yayin da aka yi wa mata dubu 1 da 799 aiki Sai Kuma mata dubu 10 da 601 suka yi bari.

Ku Karanta: Ku Tabbatar da Gwajin Jini Kafin Aure Don Kare Lafiyar ku, ‘Ya’yan Ku — Adamu Gizina

Dakta Kabo ya ce a watan janairun da muke cikin, gwamnatin jihar Kano ta kashe sama da naira miliyan 15 domin Samar da wadannan kayyaki domin kula da kananan yara da mata masu dauke da juna biyu kyauta a asibitocin jiha.

Ya Kuma bukaci kwamitin kula da rabon kayayyakin da su Kara jajircewa wajen Sanya idanu domin ganin ana amfani da kayan kamar yadda ya kamata.

Ku Karanta: Za Mu Cigaba Da Bada Gagarumar Gudun Mowa a Bangaren Lafiya — Aminu Ado

Shugaban hukumar ya Kuma bukaci sauran al’uma musamman masu hannu da shuni gami da sauran kungiyoyi da su tallafawa yunkurin gwamnati a sha’anin inaganta lafiya musamman ga mata da kananan yara.

Ya Kuma yabawa Asusun kula da lafiya na jiha bisa tallafawa Shirin a kowane wata.

Leave a Comment