Labaran Jiha Muhalli

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Feshin Maganin Kwari A GTC Ungogo

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SANI MAGAJI GARKO

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da feshin maganin Kwari a makarantun sikandire a wani mataki na yaki da kananan cututtuka a fadin jihar.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Alhaji Nasiru Sule Garo ya ce an kaddamar da feshin ne domin yaki da kananan cututtuka musamman cutar zazzabin cizon sauro da yake damun al’umma a wani taron da aka gudanar a sikandiren horar da harkokin kere-kere dake yankin karamar hukumar Ungogo “(Government Technical College GTC Ungogo)” dake Kano.

Nasiru Sule Garo ya ce, bayan kaddamar da aikin, gwamnatin jihar Kano zata tabbatar anyi feshin a dukkanin makarantun kwana da makarantun tsangaya dake Kano domin yaki da kananan cututtuka a makarantun sikandiren.

“Munzo wannan makaranta ne domin mu kaddamar da feshin maganin sauro da kula da Beraye, Micizai da sauran Kwari da zasu iya cutar da al’umma, wannan feshi yakamata ace ana yinsa duk shekara, amma munji ana samun lauje cikin nadi, amma muna tabbatar mu a wannan gwamnatin ta injiniya Abba Kabir Yusuf, gwamna sarkin aiki ya tabbatar mana da cewa duk abinda da aka amince gwamnatin zata yi, to a yi duk yadda za’ayi domin aiwatar da aikin don cigaban mutanen Kano,” inji Nasiru Garo.

Kwamishinan ya ce matukar gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta cigaba da rike madafun iko, gwamnatin zata tabbatar anyi feshin maganin a kowacce shekara a ciki da wajen Kano don inganta lafiyar alummar jihar.

Ya kuma bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da aikin feshin yayi nasara, yana mai cewa dukkan ayyukan gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf tana yun su ne don cigaban al’ummar da suka zabe ta.

A jawabinsa, kwamishinan ilimi na jihar Kano Umar Haruna Doguwa wanda shugaban makarantun sikandiren kimiya da fasaha na jihar Kano ya wakilta ya yabawa gwamnatin Kano bisa farfado da shirin a makarantun sikandiren jihar da ya dade bawa gudanarwa a cikin su.

Shugaban makarantun sikandiren wanda darakta a hukumar Alhaji Garba Ahmed ya wakilta ya bada tabbatar maaikatar ilimi da hukumar na ganin shirin ya samu nasara domin kula da lafiyar daliban hukumar.

A jawabinsa na godiya, shugaban makarantar sikandiren ta GTC Ungogo Malam Mikail Hussain ya ce feshin yazo dai-dai a lokacin da ake bukatar sa laakari da yadda daliban makarantar suki fama a cutar zazzabin cizon sauro a yan baya-bayan nan.

Leave a Comment