Ilimi

Gwamnatin Kano Ta Cika Alkawarin Biyan Kuɗin Makarantar Daliban BUK

Written by Pyramid FM Kano

Daga: YAKUBU GWAGWARWA

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala biyan kuɗin makaranta ga dalibai yan asalin jihar dake karatu a jami’ar Bayero dake Kano.

Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Kabiru Haruna Getso ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

Yace, gwamnatin ta biya akalla Naira Miliyan 700 ga dalibai sama da dubu 7 domin su sami damar cigaba da karatun su.

“Dama gwamnan Abba Kabir Yusuf yayi alkawarin biya musu kudin jiya Talata cikin ikon Allah ya cika wannan alkawari, don haka ɗaliban da abun ya shafa zasu iya zuwa jami’ar domin kara cike-ciken da suka dace don cigaba da karatun su”. A cewar Kabiru Getso.

Sakataren zartarwar ya kuma yabawa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya damu da ganin matasan jihar Kano sun sami ilimi mai inganci don kyautata rayuwar su.

Leave a Comment