Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Kano Ta Bayyana Ilimi A Matsayin Abu Na Farko Da Zata Bawa Kulawa Ta Musamman

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a yayin bikin raba kayan koyo da koyarwa ga makarantun Firamare da Sakandire dake fadin jihar Kano.

Gwamnan ya ce, samar da wadannan kayayyaki zai taimaka kwarai ga makarantun jihar Kano wajen dawo dasu hayyacinsu ya kuma bukace su dasuyi amfani da kayayyakin da aka basu ta hanyar da ya dace.

Daga bisani ya bada umarnin da a kafa kwamiti don tantance malaman da suka bada gudummawarsu wajen koyar da dalibai a jihar Kano wato yan BESDA yace nan da mako biyu gwamnati zata sasu a sahun maaikatan jihar Kano.

Daya ke nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam Gwarzo yaja hankalin dalibai da su dage wajen neman ilimi ya kuma bukace su dasu zama jakadu nagari a duk inda suke.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano ya bamu labarta mana cewar, shugaban majalisa na jihar Kano Jibrin Ismail Falgore ya ce, majalisa a shirye take wajen bawa gwamnatin jihar Kano hadin kai da ba da koyarwa a dukkan makarantu na jihar.

Leave a Comment