Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Jihar Kano Zata Samar Da Sabuwar KAROTA Domin Bunkasa Harkokin Sufuri a Fadin Jihar.

 

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na kyautata alaka tsakanin jami’an hukumar KAROTA da masu sufuri ta yadda al’umma zasu daina ganin baiken hukumar da mummunar kama a fadin jihar.

Shugaban hukumar KAROTA na jihar Kano injiniya Faisal Mahmud Kabir ne ya jaddada hakan a zantawarta da manema labarai a ofishinsa dake nan Kano.

Shugaban ya bayyana cewar ya riski hukumar a yanayi mara dadi wanda daga cikin motocin aiki
guda sittin da hudu da hukumar ke dasu guda takwas ne kawai suke aiki.

Ya kuma bayyana cewar sun riski hukumar ne a halin da alumma suke yi mata kallon azzaluma wadda take yiwa alumma kwace da kuma kwashe kayansu.

Kazalika ya koka kan yadda ya zagaya wasu daga cikin tashoshin motocin dake jihar nan inda yaga anyi gine-ginen da ba bisa ka’ida ba aka kuma mallakawa wasu shafaffu da mai a jihar.

Don haka ya yi alwashin dawo da martabar hukumar kamar yadda take tun farkon kafa ta a zamanin gwamnatin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.

Ya kara da cewar zasu rika horas da jami’ansu ta yadda zasu kware wajen tafiyar da aikinsu da kuma kyautata alaka tsakanin su da shugabanni da ma al’ummar jihar nan.

Leave a Comment