Da Dumi-Dumi

Gwamnatin jihar Kano zata hada hannu da kungiyar yan vijilanti wajen murkushe matsalar tsaro a fadin jihar

From: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na tallafawa kungiyar vigilante domin samar da cikakken tsaro a fadin jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir yusuf ya furta hakan a yayin da kungiyar yan vigilante karkashin jagorancin shugabanta na jihar Kano Kwamanda Alhaji shehu Rabiu suka kawo masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin jihar.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar kungiyar vigilante ni’imace ga al’ummar jiharnan inda ya yaba musu bisa tunkarar kalubalen tsaro dake addabar jiharnan sama da shekaru arba’in.

Ya kuma yaba musu bisa sadaukar da kai da suke yi wajen hana idanunsu barci domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Kazalika, ya basu tabbacin gwamnatinsu wajen hada hannu kafada da kafada da yan kungiyar wajen murkushe matsalar tsaro da kuma basu tallafi da kayan aiki domin saukaka musu wajen gudanar da aikinsu a fadin jihar nan.

Shima a nasa jawabin kwamandan Rundunar na jihar Kano Alhaji shehu Rabiu ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar inda yace lokacin Gwamna Dakta Rabiu Musa kwankwaso ya tallafawa kungiyar da motocin aiki guda arba’in da shida.

Ya kuma baiwa mataimakin gwamnan tabbacin cewar Rundunar su a shirye take ta tunkari kowanne irin kalubalen tsaro a fadin jihar nan.

Ya kuma kara da cewar yana daga cikin kokarin kungiyar wajen samun saukin kwacen Wayoyin hannu da kuma haura gidaje a fadin jihar nan.

Wakilinmu ya ruwaito cewar daga cikin Ayarin mataimakin gwamnan akwai Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar da sauran jiga jigan gwamnati

Leave a Comment