Labaran Jiha

Gwamnatin Jihar Kano Zata Hada Hannu Da Kananan Hukumomi 44 Domin Ciyar Da Jihar Kano Gaba

Written by Pyramid FM Kano

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na yin aiki kafada da kafada da Daraktocin kananan hukumomin jiharnan 44 domin gudanar da managartan tsare-tsare da zasu bunkasa cigaban jihar Kano.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne a madadin gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya furta hakan a yayin taro da Daraktocin kananan hukumomin jihar a ofishinsa dake ma’aikatar kananan hukumomin ta jihar Kano.

Mataimakin gwamnan wanda yake shine Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu ya bukaci Daraktocin kan su tashi tsaye wajen daukar nauyin da ya rayata a wuyansa tare da zaburar da ma’aikata kan su kasance a bakin aikinsu a koda yaushe domin marawa gwamnati ta cimma nasarar da aka sanya a gaba daya fadin jihar nan.

Ya kuma kwatanta su a matsayin jakadu nagari da ake fatan zasu taimaka wajen ciyar da tsare-tsaren gwamnati gaba.

Shima anasa bangaren Shugaban kungiyar Daraktocin kananan hukumomin jiharnan kuma Daraktan karamar hukumar Gwale Auwalu Makama Danbatta yayi alkawarin yin duk maiyiwuwa wajen marawa tsare-tsaren gwamnati baya domin ciyar da jihar nan gaba.

Ya kuma jaddada goyon bayan su ga Kwamishinan inda yace suna da yakinin zai bunkasa kananan hukumomin jiharnan 44.

Leave a Comment