Da Dumi-Dumi

Gwamnatin Jihar Kano zata hada hannu da jami’o’i masu zaman kansu domin bunkasa sha’anin ilimi a fadin Jihar Kano

 

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta Sha alwashin hada hannu tare da baiwa jami’o’i masu zaman kansu hadin kai da goyon baya domin bunkasa sha’anin ilimi a fadin jihar nan.

Mataimakin gwamnan Jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a madadin gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir yusuf ne ya yi wannan alwashin yayin da ayarin jami’ar Skyline karkashin jagorancin shugabanta Ajid Kumar suka kawo masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin jihar nan.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsu ta sanya ilimi a matakin farko da na biyu da na uku domin shine kashin bayan cigaban kowacce al’umma.

Don haka, ya basu tabbacin gwamnatinsu wajen hada hannu kafada da kafada domin bunkasa sha’anin ilimi a fadin jihar nan.

Shima anasa bangaren Shugaban Jami’ar Skyline Ajid Kumar ya ce, a shekarar 2018 ne hukumar jami’o’i ta kasa ta basu lasisin gudanar da harkokin jami’ar sannan kuma ta sahale musu yin kwasha kwashan digiri na daya zuwa na uku.

Sannan ya baiwa mataimakin gwamnan jihar tabbacin cewar ingancin da karatun jami’ar yake dashi a halin yanzu na nuni cewa daliban jiharnan zasu koyi karatu daidai da na kasashen duniya.

Daga cikin ayarin da suka kawo ziyarar akwai Daraktan harkokin kasuwanci na jami’ar.

Leave a Comment