Labaran Jiha

Gwamnatin Jihar Kano Ta Zabtare Kudin Manyan Makarantun Jihar Da Kaso Hamsin Cikin Dari

Written by Pyramid FM Kano

Gwamnatin Jihar Kano Ta Zabtare Kudin Manyan Makarantun Jihar Nan Da Kaso Hamsin Cikin Dari Domin Ragewa Iyaye Radadin cCire Tallafin Man Fetur Da Gwamnatin Tarayya Tayi.

 

From: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

 

Gwamnatin jihar Kano a kokarinta na ragewa al’ummar jihar nan radadin rayuwa ta zabtare kudin manyan makarantun jihar da dalibai ke biya duk shekara.

 

Kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Yusuf Ibrahim Kofar-Mata ne ya furta hakan a zantawarsa da manema labarai a birnin Kano.

 

Ya bayyana cewar, gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zabtare kaso hamsin cikin dari na kudin da dalibai ‘yan asalin jihar nan ke biya a manyan makarantun dake fadin jihar domin ragewa iyaye radadin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya tayi a fadin kasarnan.

 

 

Ya kuma bayyana cewar, daga cikin makarantun da zasu ci gajiyar tallafin akwai Jami’ar kimiyya da fasaha ta Dangote, Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Jami’ar Horas Da Malamai ta Sa’adatu Rimi, Kwalejin Koyar da Shari’a ta Malam Aminu Kano, Kwalejin fasaha ta jihar Kano, kwalejin Koyar Da Aikin Gona ta Audu Bako dake Dambatta, Kwalejin tayar da komadar karatu ta Dakta Rabiu Musa Kwankwaso dake Tudun Wada da kuma Kwalejin tayar da komadar karatu ta jihar Kano Wato CAS.

 

 

Kazalika, kwamishinan ya kara bayyana cewar, gwamnan ya bukaci daliban da suka amfana da wannan tallafi kan su zage damtse wajen mayar da hankalinsu kan karatunsu domin zama jakadu nagari a fadin jihar nan.

 

 

Wakilinmu ya ruwaito cewar gwamnatin jihar Kano zata tura zakakuran dalibai dubu daya da daya karatu kasashen ketare a wannan shekarar.

Leave a Comment