Nishadi

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi alwashin Farfado Da Martabar Wasanni Tun Daga Tushe Domin Ciyar Da Rayuwar Matasa a Fadin Jihar nan

 

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin farfado da martabar wasanni tun daga tushe domin ciyar da rayuwar matasa gaba a fadin jihar.

Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin wasanni da matasa na jihar nan Alhaji Yusuf Imam Shu’aibu ne yayi wannan alwashin a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan Kano.

Yusuf Imam ya bayyana cewar lokacin farkon Kama aikinsa ya tarar harkar wasanni a cikin mummunan hali take ta yadda ba zata taba amfanar matasan jiharnan ba.

Don haka ya lashi takobin farfado da martabar wasanni tun daga tushe, inda yace zai yaki dabi’ar nan ta yin cushen ‘yan wasa ko wani ya kawo nasa yace sai an tafi dashi ba tare da cancantarsa ba.

Sannan kuma ya kara da cewa duk wani fili da ‘yan shaye-shaye suke fakewa aciki afadin ungunwannin jihar nan zasu hada hannu da kamfanoni wajen sanya kayayyakin wasanni kama daga kwallon kafa, kwallon kwando, kwallon hannu da dangoginsu domin matasan yankunan su amfana.

Kazalika, yace zasu yi duk maiyiwuwa wajen inganta kungiyoyin kwallon kafa na cikin gida dake kananan hukumomin jiharnan 44 ta yadda zasu rika samar da gogaggun matasa wanda zasu rika tura su kasashen turai domin wakiltar jiharnan dama kasa baki daya.

Yusuf ya kuma bayyana cewar yanzu haka sun fitar da wani sabon tsarin tattara bayanan masu sana’o’i dake nan jiharnan domin sanin ta yadda zasu taimaki mai sana’a domin bunkasa walwalar matasa a fadin jihar nan.

Leave a Comment