Da Dumi-Dumi

Gwamnatin jihar Kano ta yi alwashin farfado da martabar ilimi tun daga tushe.

From: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na bunkasa shaanin ilimi a fadin jihar nan.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya jaddada hakan a yayin kaddamar da jarabawar NECO wanda ya gudana a dakin taro na kwalejin Rumfa dake nan kano.

Mataimakin gwamnan wanda yake jawabi a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir yusif ya bayyana cewar gwamnatinsu za ta sanya ilimi a sahun farko kuma abu nafarko wajen gudanar da ayyukanta.

Ya kuma bayyana cewar ilimi shine tushe kuma ginshikin cigaban kowacce alumma kasancewar kasashen da suka cigaba a duniya da ilimi suka yi amfani wajen gina cigabansu bawai da albarkatun kasa ba.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya kuma koka kan halin da makarantu suka tsinci kansu a ciki musamman rashin kujerun zama da kuma kayayyakin aiki inda ya bada tabbacin cewar gwamnatinsu zata yi duk maiyiwuwa wajen ganin ta dawo da martabar ilimi yadda yake tun daga tushe.

Mataimakin gwamnan ya kuma bukaci daliban da Zasu zauna jarabawar kan su jajurce wajen ganin sun yi nasarar lashe jarabawar domin zama jakadu nagari wanda jiharnan za tayi alfahari dasu.

Shima anasa jawabin mai rikon mukamin Sakataren ilimin makarantun sakandire Hamisu Muhammad Gwagwarwa ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa bijiro da managartan tsare tsare da Zasu bunkasa cigaban ilimi a fadin jihar nan tare da yiwa daliban da Zasu zauna jarabawar fatan samun nasarar jarabawar su.

Wakilinmu na ofishinsa mataimakin gwamnan jihar Kano shehu Suleiman Sharfadi ya ruwaito cewar taron ya samu halartar Kwamishinan ilimi da Daraktan hukumar K. E. R. D d shugaban kwalejin Rumfa da sauran malaman makarantar.

Leave a Comment