Labaran Jiha

Gwamnatin Jihar Kano Ta Tallafawa Masu Bukata Ta Musamman

Written by Admin

By: ADAMU DABO

Gwamnan jihar Kano Alh.Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da Bada tallafi ga masu bukata ta musamman dake fadin kananan hukumomi arba’in da hudu na Jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya kaddamar da tallafin ne a dakin taro na coronation dake gidan gwamnatin jihar.

Yusuf ya ce tallafin na naira dubu ashirin ashirin ga masu bukata ta musamman su kimanin dubu biyu na daga cikin alkawarin da gwamnatisa ta Yiwa masu bukata ta musamman

A nata jawabin kwamishinar ma’aikatar mata da kananan yara da masu bukata ta musamman Hajiya Aisha Lawan Saji ta godewa gwamnatin Kano bisa wannan tallafi da gwamnatin jihar Kano da Yi karkashin ma’aikatar ta.

Haka zalika Shugaban masu bukata ta musamman na Jihar Kano Engr.
Muhammad Musa shaba ya bayyana farin cikinsa ga gwamna bisa wannan tallafi.

Daga karshe, taron ya samu halattar manyan kusoshin Gwamnatin jihar Kano ciki harda mataimakin gwamnan jihar Kano Comr.Aminu Abdussalam Gwarzo.

Leave a Comment