Ilimi

Gwamnatin Jihar Kano Ta Sha Alwashin Farfado Da Harkokin Ilimi A Fadin Jahar Baki-daya

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Alwashin ya fitone daga bakin kwamishinan ilimi na jahar Kano Alh. Umar Haruna Doguwa a yayin wani taro na musamman domin taya al’ummar Jihar Kano dama kasa baki daya murnar cika shekaru sittin da uku da samun ‘yancin kasa wanda ya guda a gidan Gwamnatin jihar Kano.

Doguwa ya ce gwamnatin jihar Kano a karkashin Eng. Abba Kabir Yusuf, ma’aikatar ilimi ta dora damba wajen ganin ilimi ya farfardo musamman na firamari dana sakandire a fadin jihar Kano.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano ya ruwaito mana cewar, taron ya samu halartar tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Kano Prof. Hafizu Abubakar da prof. Munzali Jibril da shuwagabanin makarantu daban daban dake fadin jihar Kano.

Leave a Comment