Da Dumi-Dumi Ilimi

Gwamnatin Jihar Kano ta Sha Allwashin Farfado Da Makarantun ilimi Mai zurfi Domin Bunkasa Sana’o’i Da Tattalin Arzikin Jihar

From: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi bisa kammala binciken halin da makarantun ilimi mai zurfi suke ciki a yunkurin gwamnati na farfado da su.

Mataimakin gwamnan Jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir yusuf ya yi wannan yabon yayin kwamitin binciken makarantun ilimi mai zurfi karkashin jagorancin shugaban kwamitin Farfesa Aminu Suleiman suka kawo rahoton da kwamitin nasu ya kammala.

Mataimakin gwamnan ya yaba musu bisa kammala wannan bincike nasu wanda shine kwamiti na farko daya gabatar da rahotonsa a duk kwamitocin da aka kafa a wannan gwamnatin.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar wadannan cibiyoyin, cibiyoyi ne masu dadadden tarihi kuma masu matukar muhimmanci wanda da sun samu kulawa shekaru takwas da suka gabata da rayuwar matasan jiharnan tayi nisa fiye da yadda ake tunani.

Kwamared Aminu Abdussalam ya koka kan yadda gwamnatin baya tayi biris da irin wadannan cibiyoyi wanda da sun samu kulawar da ta dace da tuni harkokin sha’anin sana’o’i sun bunkasa ta yadda ba za’a samu masu zaman kashe wando a fadin jihar nan ba.

Kazalika, ya baiwa ‘ya’yan kwamitin tabbacin goyon baya ta yadda aikinsu zai samu gagarumin cigaba a fadin jihar Kano.

Shima anasa jawabin, shugaban kwamitin farfesa Aminu Suleiman ya bayyana cewar farfado da irin wadannan makarantu a jihar nan zai bunkasa rayuwar al’umma da kuma tattalin arzikin su.

Ya kuma kara da cewa irin wadannan makarantu idan aka farfado dasu zasu amfani mutanen da suka yi karatu dama wadanda basu yi karatu ba kai har ma da wadanda ke shirin yin ritaya ko ma suka yi ritayar daga aikin gwamnati.

Wakilinmu ya ruwaito cewar daga cikin mahalarta taron akwai Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata da sauran wakilan kwamitin.

Leave a Comment