Da Dumi-Dumi

Gwamnatin jihar Kano Ta Nanata Kudirinta na horas da jami’anta kan sanin makamar aiki a fadin Jihar Kano

 

From: SHEHU SULEIMAN SHARFADI
Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya jaddada hakan a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir yusuf yayin kammala taron karawa juna sani na kwanaki uku da aka shiryawa ma’aikatan gidan gwamnatin jihar wanda ya gudana a gidan Mambayya dake kano.

Mataimakin gwamnan ya bayyana farin cikinsa bisa yadda masu cin gajiyar shirin suka nuna kwazonsu yayin bitar ta kwanaki uku.

Ya kuma basu tabbacin cewar gwamnatinsu zata basu hadin kai da goyon baya dari bisa dari domin ciyar da sha’anin gudanar da mulki gaba a fadin jihar nan.

Kwamared ya kuma hore su da suyi amfani da ilimin da suka koya a wuraren aikinsu.

Shima anasa bangaren, Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Alhaji Shehu Wada Sagagi ya bayyana cewar rabon da ayi irin wannan bitar ya kai shekaru talatin da suka shude.

Daga nan kuma sai ya kai ziyara sabuwar cibiyar koyar da Fasahar Sadarwa dake Sakatariyar Audu Bako.

Daga nan kuma sai ya wuce zuwa Kwanar Dawaki inda ya kai ziyara sabuwar cibiyar koyar da sana’o’i da Alhaji Aliko Dangote ya gina.

Wakilinmu ya ruwaito cewar daga cikin ayarin mataimakin gwamnan akwai Kwamishinan Yada Labarai Baba Halilu Dantiye da sauran jiga jigan gwamnati.

Leave a Comment