Da Dumi-Dumi

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin gangamin yaki da cutar shan Inna a fadin jihar

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da shirin rigakafin cutar shan Inna a fadin jihar nan.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir yusuf ya kaddamar da shirin rigakafin cutar shan Inna a garin zakirai dake karamar hukumar Gabasawa .

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar wannan gangamin yaki da cutar shan Inna cigaba ne na shirin wanda gwamnatin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya rika yi a zamanin gwamnatin sa wanda saboda namijin aiki da aka rika yi a wancan lokacin a cikin shekara daya aka murkushe cutar aka daina jin bullarta afadin jihar nan.

Ya kuma bayyana cewar sakamakon wancan namijin aiki sai da hukumar lafiya ta duniya a shekarar 2020 ranar 25 ga watan Ogusta ta baiwa kasarnan lambar yabo kan cewar babu cutar shan Inna a fadin kasarnan.

Sai dai kuma abin takaici sai daga baya aka sake samun bullar cutar a kasarnan sakamakon sakaci da kuma rashin ko in kula da gwamnatin da ta gabata tayi a fadin jihar.

Don haka ya bukaci Shugaban karamar hukumar ya hada hannu da ofishin hakimin karamar hukumar da masarautu kama daga kan dagaci zuwa masu ungunwanni domin tabbatar da ganin cewar shirin ya samu nasara.

Shima anasa jawabin Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf yace an kaddamar da wannan shiri ne sakamakon sake samun bullar cutar a jihohi 26 a fadin kasarnan ciki har da jihohin Kano, Kaduna, Katsina da sauran jihohin Arewacin kasarnan.

Ya kuma bukaci hukumar bunkasa sha’anin lafiya ta kasa kan ta tabbatar ta samar da wadatattun allurai a fadin jihar nan domin samun nasarar shirin.

Daga karshe ya godewa mataimakin gwamnan bisa halartar wannan taron gangamin yaki da cutar Shan Inna da aka kaddamar a karamar hukumar Gabasawa.

Wakilinmu na Ofishin mataimakin gwamnan Jihar ya ruwaito cewar taron ya samu halartar Wakilin Sarkin Kano da Wakilan Hukumar lafiya ta duniya da na Asusun tallafawa kananan yara da na Gidauniyar Melinda and Gate da na Aliko Dangote da na hukumar bunkasa sha’anin lafiya da sauran kungiyoyin lafiya dake kasarnan.

Leave a Comment