Labaran Jiha

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Abinci Karo Na Biyu

Written by Pyramid FM Kano

Daga: ADAMU DABO

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da rabon kayan abinci karo na biyu ga al’ummar jihar na ƙananan hukumomi 44.

Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da kayan abincin a fadar Gwamnatin Kano.

Yusuf ya ce zata fara rabawa al’ummar  Kano ta tsakiya adadin buhhuna 105600 da suka haɗar da shinkafa da masara.

Wakilinmu dake fadar gwamnatin jihar Kano adamu Dabo ya bamu labarin cewar tun da fari a jawabinsa na maraba, shugaban kwamitin raba tallafin kayan abinci kuma sakataran gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi yayi jawabin godiya tare da godewa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewa wajen bijiro da wannan hanyar tallafin ga al’umma.

Leave a Comment