Labaran Jiha

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Manhajar Ma’aikata

Written by Admin

Daga: ADAMU DABO

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da hanyar biyan albashi ma’aikatan a yayin zaman majalissar zartarwar Karo na shabi’u da ya gudana a gidan gwamnatin jihar Kano.

Gwamna Yusuf ya Kuma bayyana yanayin manhajar biyan albashin na bai-daya da cewar zai kawo hanyoyin magance matsalolin albashi ga ma’aikatan jihar Kano.

Ya Kuma ce ya zama wajibi duk wani ma’aikacin gwamnati kama daga na kananan hukumomin dana jiha kowa sai ya yi rijista da wannan manhajar biyan albashi.

A yayin zaman majalissar zartarwar Karo na 12 akwai sakataran gwamnati shugaban ma’aikatan jiha da akanta na jihar Kano da sauran kwamishinoni.

Leave a Comment