Labaran Jiha

Gwamnatin Jihar Kano Ta Jinjinawa Dan Majalisa Bisa Rabon Kayan Tallafi A Mazabarsa

Written by Admin

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar kano ta yabawa dan majalisar dokokin jihar kano mai wakiltar karamar hukumar fagge Alhaji Tukur Muhammad bisa rabon kayan tallafin kayan sanaoi ga mata dubu daya da dari biyu a mazabarsa.

Mataimakin Gwamnan jihar nan kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne amadadin Gwamna Alhaji Abba kabir yusuf yayi wannan yabon yayin kaddamar rabon kayan tallafin ga wasu iyaye mata a karamar hukumar fagge.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewar rabon kayan sanaoi a halin yanzu yana da matukar muhimmanci ta yadda zai taimaka musu wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.

Daganan, sai kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya ja hankalin wadanda suka ci gajiyar tallafin kan su tashi tsaye wajen rungumar sanaoi domin dogaro da kansu.

Wakilinmu ya ruwaito cewar, taron ya samu halartar shugaban jam’iyyar NNPP da kwamishinoni da kantomomi da kuma, manyan jiga-jigan gwamnatin jihar nan.

Leave a Comment