Da Dumi-Dumi

Gwamnatin jihar Kano Ta Jaddada Kudirinta Na Hada Hannu Da Kungiyoyi Masu Zaman Kansu Domin Bunkasa Sha’anin lafiya a jihar

 

Daga: SHEHU SULEIMAN SHARFADI

Gwamnatin jihar Kano ta nanata kudirinta na hada hannu da kungiyoyi masu zaman kansu domin bunkasa sha’anin lafiya da tattalin arziki na zamani.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne a madadin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya furta hakan a yayin da Gidauniyar Melinda and Gate ta kawo masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin jihar.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsu nayin duk mai yiwuwa wajen ganin ta bunkasa sha’anin lafiya tun daga matakin farko a jihar nan.

Ya kuma bayyana cewar jihar Kano na bukatar Allurar riga kafi kimanin miliyan shida domin inganta sha’anin lafiya tun daga tushe.

Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya yabawa Gidauniyar bisa tallafi da kuma taimakon da take a bangarori da dama musamman sha’anin lafiya.

Shima anasa bangaren jagoran Gidauniyar Melinda and Gate na kasarnan Jeremy Zungurana yace sun kawo ziyarar ne domin jaddada yarjejeniyar fahimtar juna da Gidauniyar ta kulla da Gwamnatin jihar nan shekaru goma sha biyu da suka gabata.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar bisa kokarinta a sha’anin lafiya tare da gode mata bisa alkawarin da ta dauka na basu hadin kai da goyon baya dari bisa dari a fadin jihar Kano.

Wakilinmu ya ruwaito cewar daga cikin mahalarta taron akwai Kwamishinan lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf da Daraktan Lafiya da Manyan Sakatarori na ofishin mataimakin Gwamna.

Leave a Comment